Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 496 Nan Gabas Dubu Suna Ta Mutuwa Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 496 Nan Gabas Dubu Suna Ta Mutuwa Lyrics

 

1
Nan gabas dubu suna ta mutuwa
Ba su da maganar rai
Nan yamma dubu suna ta kira
Na mu da maganar rai.

KORUS
Nan gabas, da yamma, arewa da gusum
Mu tafi, mu tafi da maganar Allah
Mu tafi, mu tafi, suna jiranmu can
Mu tafi, mu tafi, don su sami tsira.

2
Arewa kuma dubu ke jira
Ba su da sanin ceto
Nan gusum suna ta biɗa
Biɗan salamar Allah.
Korus

3
Ga tafiyar dangi cikin wuta
Ҡarƙarshin shari’a
Fushin Allah bisansu zamne
Muna da ƙofar rai.
Korus

Exit mobile version