Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 493 Mutuwar Yesu Lyrics
1
Mutuwar Yesu ta sa ina da bege na rai
Ya tashi kuwa da rai ya koma wurin Uba.
KORUS
Mata: “Mafasa biyu.” (Maza: “Masu kisa.”
Mata: “An giciye shi.” (Maza: “Tare da shi suke.”
Mata: “Ɗaya hannun dama.” (Maza: “Mai azanci.”
Mata: “Ɗaya hannun hagun.” (Maza: “Marar azanci ne sh.i”
Duka: “Mutuwar Yesu ta sa ina da bege na rai”
2
Sun iso Golgotha inda za su giciye shi
Su ka kuwa giciye shi tare da masu laifi.
Korus
3
Bayan da sun gama sun raba tufafinsa
Sun rubuta wannan Yesu Sarkin Yahudawa.
Korus
4
Ƴan’uwa masu bi ran Ista ranar ceto
Wa mu ke bi a yau Yesu Kristi ko Shaiɗan
Korus