Skip to content

info@example.com

Treasure Hymns – Hausa

  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page
  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page

Hymn 492 Mutane Sun Far Yawaita a Duniya Lyrics

  1. Home   »  
  2. Hymn 492 Mutane Sun Far Yawaita a Duniya Lyrics

Hymn 492 Mutane Sun Far Yawaita a Duniya Lyrics

January 10, 2026 treasurehymnsLittafin Wakoki Hausa Hymns

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 492 Mutane Sun Far Yawaita a Duniya Lyrics

 

1
Mutane sun fara yawaita a duniya,
Sun cika ƙasashe daga gabas har da yamma,
Kowa da sunansa da harshe dabam-dabam,
Sun bi ta hanyar duniya, sun mance da Uban.

KORUS-1
Zan hallakada duniya,
In ji Ubangiji,
Zan aiki ruwan sama
Cikin wannan kwanaki.

2
Duk tunani da shawara ƴan Adam lala ne,
Ba wanda ya kula da abin da Allah ya ce,
“Na tuba da na yi mutum da dukan masu rai.
Zan shafe su da dabbobi har dukan tsuntsaye.”
Korus-1

3
Akwai mutum, sunansa Nuhu, mai adalci ne,
Ya sami tagomashi a gaban Ubangiji,
Kullum yana tafiya tare da Allah ne,
Tare da shi Allah ya yi babban alkawali.

KORUS-2
Ka shiga cikin jirgi,
Da kai da ƴaƴanka,
Zan hallakada duniya
Da ruwan tufana.

4
Shakara ɗari biyu Nuhu ya yi ta wa’azi
Ya yi ta shirya jirgi ko bai gane da abin,
Mutane sun yi dariya. “Ya hauka” duk sun ce,
Amma Nuhu bai kula ba, biyayya shi ke dai.
Korus-2

5
Nuhu ya biɗa bisashe da tsuntsaye biyu biyu,
Sun shiga cikin jirgin nan tare da ƴaƴansa,
Allah ya rufe ƙofa, ruwan tsufana ya zo,
Ya rufe fuskar duniya har dukan duwatsu.

KORUS-3
Mutane duk sun mutu,
Don ba su tuba ba,
Amma ya ceci Nuhu
Don ya bada gaskiya.

6
Ku mutane ku saurara abin da ya faru,
Ku juyo daga duhunku, ku tuba tun yanzu,
Ku shiga cikin ƙamnar Yesu, roƙi gafara,
Allah za ya ji ku, za ya buɗe ƙofa kuwa.

KORUS-4
Ku shiga cikin jirgi,
Bai rufe ƙofa ba,
Amma idan kun kira
Lalle za ku yi makara.

Post navigation

Previous: Hymn 179 Na Ji Kiranka, Ya Mai Cetona Lyrics
Next: Hymn 484 Mun Gode Allah Ubangiji, Domin Ƙamnarka Lyrics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
  • Hymn 215 A Cikin Duniyan Nan Yanzu Lyrics
  • Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
  • Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
  • Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • January 2026

Categories

  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Uncategorized
Proudly powered by WordPress | Theme: goldy-mex by inverstheme.
Go to mobile version