Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 491 Muna Zuwa Wurin Yesu Mai Ceto Lyrics
1
Muna zuwa wurin Yesu Mai Ceto
Domin shiga aikinsa
Shi ya kira mu mu yi ta wa’azi
Ko’ina a duniya.
KORUS
Yesu shi ne shugaba
Shi ne mai ƙamnar mutane.
Za mu taya shi, mu nemansu
Don su sami gafara.
2
Ko minene Yesu shi ya ce mu yi
Za mu yi da zuciya ɗaya
Za mu yi biyayya cikin abu duk
Za mu yi ta wa’azi.
3
Shi ya ce mu bar duk zunubi na da
Mu tafi da tsabta rai
Ko ya ce ya so abin da namu ne.
Za mu ba shi nan da nan.
