Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 49 Ubangiji Yesu, Ina Roƙonka Lyrics
1
Ubangiji Yesu, ina roƙonka,
Kai ne na ke kira, ina jiranka.
2
Ga ni nan gabanka, bawanka na ke.
Kai ne ka fanshe ni da jininka dai.
3
Daga halin duniya raba ni yanzu
Gaskiya da ƙauna ina nemansu.
4
Koya mini sani, sanin nufinka.
Ni dai marar iko, ba ni ikonka.
5
Amshi mulkin raina, karƃi zuciyata.
Ba na jin ta wani, sai maganarka.
6
Hali irin naka ni ke so in yi.
Ruhunka Mai Tsarki, cika ni da shi.