Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 489 Muna Murnar Haifuwar Yesu Lyrics
1
Zamanin da Almasihu ya zo…duniya
An haife shi mai cetonmu…Baitalahmi
Haifuwarsa abin mamaki ne…sosai
Don cika nufin Allah
KORUS
Yau muna murna haifuwar Yesu
Domin shi Mai Cetonmu ne
Sai ku zo mu yi masa sujada
Shi Sarkin Salama ne.
2
Masu hikima a cikin duniya…duka
Ku daina zurfin tunani…cikin zuciyarku
Ku nemi ceto a wurin Yesu Kristi
Shi zai baku taimako
Korus
3
Makiyaya suna tsoron garken..su fa
Haske ne ya kewaye su…cikin daren nan
Aka shaida masu ƙaunar Allah…sun ji
Sai sun cika da murna.
Korus
4
Maza da mata har da matasa…duka
Tsofoffi yara sai ku zo…wurin Yesunmu
Zo mu guida Yesu Kristi…Almasihu
Yau ne ranar haifuwarsa.
Korus
