Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 487 Muna Cikin Tafiya, Tafiya Zuwa Sama Lyrics
1
Muna cikin tafiya, tafiya zuwa sama.
Menene za mu ƙunsa a hannunwanmu
don saduwa da Yesu?
Saduwarmu, menene za mu ƙunsa
A hannunwanmu don saduwa da Yesu?
2
Mai yin zina, menen za ka ƙunsa
A hannunwanka don saduwa da Yesu?
Mai yin sata, kana cikin tafiya
Tafiya zuwa sama, menene za ka ƙunsa
A hannunwanka don saduwa da Yesu
3
Mai yin tsafi, menene za ka ƙunsa a
Hannunwanka don saduwa da Yesu?
Mai yin ƙarya, kana cikin tafiya,
Tafiya zuwa sama, menene za ka
Ƙunsa a hannunwanka don saduwa da Yesu ?
4
Mai kormoto, menene za ka ƙunsa
a Hannunwanka don saduwa da Yesu?
Mai yin fushi kana cikin tafiya,
Tafiya zuwa sama, menene za ka
Ƙunsa a hannunwanka don saduwa da Yesu?
5
Mai yi gulma, menene za ka ƙunsa
a hannunwanka don saduwa da Yesu?
Mai yin kisa, kana cikin tafiya,
Tafiya zuwa sama, Menene za ka ƙunsa
a hannunwanka don saduwa da Yesu ?
6
Mai maza biyu, menene za ki ƙunsa
a hannunwanki don saduwa da Yesu?
Mai-mata biyu. kana cikin tafiya,
Tafiya zuwa sama, menene za ka ƙunsa
a hannunwanka don saduwa da Yesu?