Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 486 Mun Gode Maka Yesu, Ɗan Maƙamnacinmu Lyrics
1
Mun gode maka Yesu, Ɗan Maƙamnacinmu
Do kana ta lura da mu, ɓatattun tumaki.
KORUS
Yabo ya tabbata, ya tabbata ga Yesu
Yesu, Yesu, sunanka da daɗi.
Karɓi roƙon bayinka domin su sami tsira.
2
A cikin sunan Yesu muna kurkusa ga Allah
Shi wanda ya mutu domin dukan mutane.
Korus
3
A cikin yaƙin nan muna da aboka gabanmu.
Kai ne za ka taimake domin mu ci magabta.
Korus
4
In na tuna, in na tuna da ƙamnar Almasihu
Sai hawaye na zuba domin na ɓata hanya.
Korus
