Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 485 Mun Gode Maka Yesu Ɗan Uba Maƙaunacimmu Lyrics
1
Mun gode maka Yesu
Ɗan Uba maƙaunacimmu,
Don kana ta lura da mu ƃatattu na duniya.
KORUS
Yabo ya tabbata. ya tabbata ga Yesu.
Yesu, Yesu sunanka da daɗi,
Karƃi roƙon bayinka
Domin su sami tsira.
2
A cikin yaƙin nan
Muna da su abokan gaba.
Kai ne za ka taimakemu har mu ci magabta.
Korus
3
Ko mun mutu a yaƙin nan
La karƃi rayukanmu.
Ba don ayukanmu ba, domin mu kasassu ne.
Korus