Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 484 Mun Gode Allah Ubangiji, Domin Ƙamnarka Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 484 Mun Gode Allah Ubangiji, Domin Ƙamnarka Lyrics

 

1
Mun gode Allah Ubangiji,
Domin ƙamnarka,
Yadda kai ka bada Ɗanka Yesu
Domin cetonmu.

KORUS
I, muna yin roƙo
Ya Ubangijinmu,
Ka ji addu’armu,
Cika mu da ƙamnarka.

2
Muna roƙo Ubangiji Yesu
Ҡara ƙamnarmu,
Mu dai ba mu cika ƙamnar juna
Yadda ka ke so.
Korus

3
Muna roƙo Ruhun Ubangiji
Cika zuciyarmu,
Cika mu da nufin yin biyayya
Da maganarka.
Korus

4
Allah Uba, Yesu Mai Cetonmu
Ruhu Mai Tsarki,
Duka uku sai ku taimake mu
Muna yin addu’a.
Korus

Exit mobile version