Skip to content

info@example.com

Treasure Hymns – Hausa

  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page
  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page

Hymn 482 Mugun Bawa Nake Lyrics

  1. Home   »  
  2. Hymn 482 Mugun Bawa Nake Lyrics

Hymn 482 Mugun Bawa Nake Lyrics

January 10, 2026 treasurehymnsLittafin Wakoki Hausa Hymns

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 482 Mugun Bawa Nake Lyrics

 

1
Mugun bawa nake, na bar tafarkin Allahna.
Na ƙi Ubangiji da ɗansa Yesu, na bi Shaiɗan na ƙi Allah .
Na shigo duniya da shan giya da yin maye.
Ina yin tsammani ina jin daɗi ina yanga da mugunta .
Ina zuwa Church ina baiko ina zakka,
Amma Ubangiji ba zai sani ba, ranar ƙarshe zan sha kunya.
KORUS
Wannan abin tausayi ne [Maza: “abin tausayi ne.”]
Ya isa ma in yi kuka [Maza: “Yi kuka ga Allah.”]
Waiyo Allah Uba waiyo Allah gani mugun bawa na lalace.
Uba ka karɓe ni gani wurinka oh ya Uba ka yi jinƙai.

2
Mugun bawa nake ni ne babban munafiki .
Ni mai adalci gaban mutane amma cikina da daci.
In ana wa’azi sai in yi kamar na damu.
Amma in an gama an komo gida sai in koma bayan gari.
To, Ubangijina ni ban bar zuwa gunka ba,
Amma na ƙi bari ayyukan duhu ranar ƙarshe babu bege.
Korus

3
Mu masu bin Yesu kada mu yi ruɗin kanmu.
Gama Ubangiji ba wawa ba ne ba a yi masa ba’a ba.
Abin da na shuka shi ne abin da zan girba.
Na san hukuncinsa ai babu shakka ranar ƙarshe zan sha kunya.
Oh, masu bin Yesu kullum sai ku tuna da ni,
Cikin addu’arku gama na zama mugun bawa na lalace.
Korus

Post navigation

Previous: Hymn 483 Mun Gode Lyrics
Next: Hymn 232 Mai Kiwona Shi Yesu Ne Lyrics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
  • Hymn 215 A Cikin Duniyan Nan Yanzu Lyrics
  • Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
  • Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
  • Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • January 2026

Categories

  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Uncategorized
Proudly powered by WordPress | Theme: goldy-mex by inverstheme.
Go to mobile version