Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 480 Mu Yi Farin Ciki Mu Yi Murna Kuwa Lyrics
1
Mu yi farin ciki mu yi murna kuwa
Don masu bin Yesu akwai nasara
Zai fyauce mu duka mu ratse sammai
Zai ciyadda ranmu da itaccen rai.
KORUS
Nasara, nasara zuwa dukan mu dai
Nasara, nasara za mu ci ta sosai
Mu zo mu bi Yesu mu yi anniya
Zai ba mu ladanmu na har abada.
2
Ga can cikin sama a rubutace
Suna na mai binsa kan farin dutse.
Ba wanda ya sani sai shi mai karɓa
Da Ubangijinmu Mai Cin Nasara.
Korus
3
Wanda ya bi Yesu Mai Ceto kaɗai
Za a ba shi tufafi da rawanin rai
Zai zamna da Kristi a kursiyinsa
Da murna mai yawa don yin nasara.
Korus
