Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 48 Kurkusa Ga Giciyenka, Kullum Dai Ka Ja Ni Lyrics
1
Kurkusa ga giciyenka, kullum dai ka ja ni.
Ceto, murna, gafara, wurin nan na samu.
KORUS
Yesu ne, Yesu ne, shi ne ya fanshe ni.
Zuciyata da muryata za su ba ka girma.
2
Da na zo da zunubi, kaya ne mai nauyi.
Tsoro, rawar jiki kuwa, Yesu ya karƃe ni.
Korus
3
Na ƙallafa raina kuwa cikin aikin Yesu,
Ba nawa adalci ba, sai adalcin Yesu.
Korus
4
Aikina nan gaba kuwa, shi ne shelar ceto,
Domin masu zunubi, in sun zo gun Yesu.
Korus
5
Can a cikin Sama fa, yabo da sujada,
Godiya ba fasawa, za mu yi wa Yesu.
Korus