Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 472 Menene Aikin Bangaskiyarmu Lyrics
1
Menene aikin bangaskiyarmu
a cikin duniyan nan?
Ba wata hanya ta samun tsira
sai dai ta wurin Yesu.
KORUS
Yesu uba yana kira,
Yana tambayarmu duk,
Menene aikin bangaskiyarmu?
Yesu yake tambaya.
2
Zo wurin Yesu ka san gaskiya.
Sai dai ka tuba yanzu.
Ba wata hanya ta samun ceto
sai dai ta wurin Yesu.
Korus
3
Ku zo mu nemi wannan gaskiya
domin mu semi ceto.
Kada mu yarda mu bi duniyan nan.
Duniya za ta ƙare.
Korus
4
Menene za ya hana ka zuwa
wurin Yesu mai~ceto?
Mai-cetonmu yana tambayarka.
Ina bangaskiyarka?
Korus
