Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 470 Mazajen Galili Lyrics
KORUS
Ku mazajen Galili, ku tsarkaka
Don mi ku ke kallo a sama?
Yadda ku ka tafiyar Yesu a sama
Haka ne zai sake dawowa.
1
Idan mutane sun ce, “Ga Kristi can !
Ga Kristi nan, kada mu gaskanta!” (2x
Maƙaryatan annabawa za su zo.
Su ruɗi mutane da yawa, kada ku gaskanta,
(Karatu: Mat 24: 4-5, 23-28
Korus
2
Idan mutane sun ce, “Ga Kristi can !
Ga Kristi nan, kada mu gaskanta.” (2x
Maƙaryatan annabawa za su zo
Su yi abubuwan al’ajabi, kada ku gaskanta
Korus
3
Idan mutane sun ce, “Ga Kristi can!
Ga Kristi nan, kada mu gaskanta” (2x
Maƙaryatan annabawa za su zo
Su ɓadda zaɓaɓɓu da yawa, kada ku gaskanta.
Korus
4
Idan mutane sun ce, “Ga shi cikin jeji !
Ga shi lolokai, kada ku gaskanta !”
Ran da ɗan mutum zai zo
Duniya duka za ta gan shi, kowa zai gaskanta.
Korus
