Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 47 Yesu Mai Alheri, Ɗan Maɗaukaki Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 47 Yesu Mai Alheri, Ɗan Maɗaukaki Lyrics

 

1
Yesu mai alheri, Ɗan Maɗaukaki,
Kristi mai tausayi, ji addu’armu.

2
Yafe laifofinmu, kwance sarƙarmu,
Karƃi dukan muIki cikin zuciyarmu.

3
Cika ranmu duka, ba mu Ruhunka,
Jawo mu, Mai Ceto, zuwa mulkinka.

4
Bi da ƙafafunmu cikin hanyarka,
Daga duhun duniya zuwa haskenka.

5
Nan kuwa cikin duniya, mu ke kiranka.
Daga cikin Sama, kasa kunnenka.

Exit mobile version