Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 467 Masu Shelar Bishara Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 467 Masu Shelar Bishara Lyrics

 

1
Mutane duka sun taurara da jin maganar Uba
Don duniyan nan ta kwace su; suna jin, amma ba aikata.
(2x

KORUS
DUK: Masu shelar bishara ko’ina da Littafi Mai Tsarki.
Ana shela mana bishara; muna ji, amma ba aikata.
Maza: Ga Pastoci, ga dattiɓai, ga malamai ko’ina,
Ga su Reverend suna faɗa mana; muna ji, amma ba a.

2
Karanta wasiƙar Yakubu sura ta ɗaya aya goma
Sha tara zuwa aya, aya ashirin da bakwai.
(2x

Korus

3
Karmu zama masu ji kaɗai, amma ba aikatawa.
In ba aikatawa ƴan’uwa, ranar ƙarshe za mu hallaka.
(2x

Korus

4
Duniyan nan tana ruɗinmu, jin daɗi za ya ƙare.
A ran da Uba zai tattara dukan hallita na duniya.
(2x

Korus

Exit mobile version