Skip to content

info@example.com

Treasure Hymns – Hausa

  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page
  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page

Hymn 466 Masoyina Yana Sama Lyrics

  1. Home   »  
  2. Hymn 466 Masoyina Yana Sama Lyrics

Hymn 466 Masoyina Yana Sama Lyrics

January 10, 2026January 10, 2026 treasurehymnsLittafin Wakoki Hausa Hymns

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 466 Masoyina Yana Sama Lyrics

 

1
Masoyina yana sama,
shi ne Yesu Ɗan Allahnmu.
Yana sama, yana shirya
wurin zama can dominmu,
saboda ni, ba ni da kowa,
ko aboki a duniyan nan.
Ruhunsa ne ya biɗa duk
ya koya mana aikinsa.

KORUS
Masu-bi ku zo, mu bi Yesu
Yesu shi ne makiyayi. (2x

Karatu: Ubanmu wanda ke cikin sama —- (Addu’ar Ubangiji

2
Ku ƴan ƙwaya ku shaida fa,
Almasihu yana zuwa.
Ku mutane, ku shaida
fa Almasihu yana zuwa.
Ku Pastoci, ku yi aniya,
ku yi aiki da aminci.
Ku je ku yi shaidar bishara,
ku je ku kawo ƃatattu.
Korus

Karatu: Masoyina, masoyina yana sama.
Shi ne Ɗan Allah wanda ya rnutu.
Sabili da zunubanmu. Ƴanuwa
Ku duba irin ƙauna da Yesu ya yi
domin mu zama masu ƙaunar juna

3
Ku matasa, ku shaida fa
Almasihu yana zuwa.
Ku yara ma, ku shaida fa
Almasmu yana zuwa.
Zumuntar mata, ku yi aniya,
Ku yi aiki da aminci,
Ku je ku shaida bishara,
Ku je ku kawo ƃatattu.
Korus

Karatu: Kamar yadda Yesu ya koya mana,
ku ƴan ƙwaya, da masu shaidar bishara.
da Pastoci, da su referan, da zumuntar mata,
ku mutane duka, ku tashi tsaye,
ku yi aikin Ubangiji fa, gama lokaci ya kusa,
Yesu yana zuwa. Babu shakka zai ba kowa ladan
aikinsa.
Allah ya taimakemu. Amin.

Post navigation

Previous: Hymn 232 Mai Kiwona Shi Yesu Ne Lyrics
Next: Hymn 464 Mai Tsarki Lyrics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
  • Hymn 215 A Cikin Duniyan Nan Yanzu Lyrics
  • Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
  • Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
  • Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • January 2026

Categories

  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Uncategorized
Proudly powered by WordPress | Theme: goldy-mex by inverstheme.
Go to mobile version