Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 465 Mai Yin Ƙarya, Ka Bar Yin Ƙaryarka Lyrics
1
Mai yin ƙarya, ka bar yin ƙaryarka.
Ka zo, ka tuba, ki zo, mu tuba
Domin mu bi Mai ceto
Mai yin tsafi, ka bar yin tsafinka,
ka zo, ka tuba. ki zo, mu tuba
domin mu bi Mai-ceto.
KORUS
Ƴan’uwana, turbaya ne muka zo.
Turƃaya ne za mu, tuƃaya ne za mu koma
Mun zo cin kasuwa, turƃaya ne muka zo,
Turƃaya ne za mu, turƃaya ne za mu koma.
2
Mai shan giya, ka bar shan giyanka
ka zo, ka tuba. ki zo, ki tuba
domin mu bi Mai ceto
Mai shan taba ka bar shan tabanka.
ka zo, ka tube, ki zo, ki tuba
domin mu bi Mai ceto.
Korus
3
Mai aure biyu, ka bar yin aure biyu,
ka zo, ka tuba, ki zo, ki tuba
domin mu bi Mai ceto
Duniya nan akwai cuta cikinta.
Akwai wahala, akwai azaba,
duniya za ta shuɗe fa.
Korus
4
Kana da mata, mai cin amanarka,
Kada ka damu, akwai shari’a
A ranar zuwan Yesu.
Kina da miji, mai cin amanarki.
Kada ki damu, akwai shari’a,
a ranar zuwan Yesu.
Korus
