Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 46 Ya Yesu, Ubangijinmu Lyrics
1
Ya Yesu, Ubangijinmu,
Wurinka muka zo yanzu.
Kai ne mai sanin cutarmu,
Kai ne mai ikon warkarwa.
2
Zunubanmu dayawa ne,
Har ba mai ikon ƙirgawa,
Sai kai kaɗai, Mai Cetonmu,
Ya Yesu Ubangijinmu.
3
Ya Makiyayin Isra’ila,
Kiyaye mu da ikonka,
Domin mu shaida ƙaunarka,
Tun daga yau har abada