Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 458 Ku Zo Mutane Duk Lyrics
1
Ku zo mutane duk
Ku furta laifofinku yau
A gaban Yesu Mai Ceto,
Shi zai yi gafara .
2
Idan da zafin kishi yau
Cikin masu bin Yesu.
Ba za su yi albarka ba
Idan da kishin nan.
3
Ƴanuwa, ku bar kishi
Ku bar ƙeta, ku bar ƙarya
Ku bar zina, ku bar gulma
Ku bi Mai Cetonmu.
4
Idan da waɗannan abu
A cikin zukatanmu yau
Me za mu ce ma Yesu
Ran da mun kai sama?
5
Shi zai ce ku tashi nan
Ku tashi nan, ku tashi nan
Shi zai ce ku tashi nan
Ni dai ban san ku ba.
6
A ranan nan sai kumya
Kumya mar-iyaka
Sai kuka mai zafi kuwa
Da cizon haƙora.
7
Masu bi, mu yi anniya
Domin ranar zuwansa
Zai ce da mu bayin kirki
Ku shiga murnarku.
8
Taimake mu, ya Yesu
Ka bi da mu da Ruhunka
Domin mu aika nufinka
Har ran da za ka zo.
9
Halleluya ga Yesu
Ga Yesu Mai Cetonmu.
Halleluya ga Yesu, halleluya Amin
Ga Yesu Mai Ceto.