Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 457 Ku Zo Mu Tafi Wurinsa, Yesu Ne Ɗan Allah Lyrics
(Kira da amsa
(Duka
Ku zo mu tafi wurinsa, Yesu ne Ɗan Allah
Shi ne ya panshe mu da jininsa
Yesu Ruhullahi, Shi ne Ruhun Allah
Wanda ya panshe mu da jininsa.
K: Musulmi da arna duk, ku zo mu tafi wurinsa.
A: Yesu ne Ɗan Allah, Shi ne ya panshe mu da jininsa.
K: Turawa da Larabawa, ku zu mu tafi wurinsa
A: Yesu ne Ɗan Allah, Shi ne ya panshe mu da jininsa.
K: Yesu Almasihu shi ya bada ransa, dalilinmu.
A: Yesu ne Ɗan Allah, Shi ne ya panshe mu da jininsa.
K: Mu mutanen Yesu sai mu bada ranmu, dalilinsa.
A: Yesu ne Ɗan Allah, Shi ne ya panshe mu da jininsa.
K: Kai fa ɗanuwanmu sai ka bada ranka, dalilinsa.
A: Yesu ne Ɗan Allah, Shi ne ya panshe mu da jininsa.
K: Ke fa, ƴaruwanmu sai ki bada ranki, dalilinsa.
A: Yesu ne Ɗan Allah, Shi ne ya panshe mu da jininsa.
K: Za mu raira waƙa, raira halleluya, dalilinsa.
A: Yesu ne Ɗan Allah, Shi ne ya panshe mu da jininsa.
K: Sai mu tada murya, sai mu tada murya, dalilinsa.
A: Yesu ne Ɗan Allah, Shi ne ya panshe mu da jininsa.
K: Za mu ga Ubanmu, za mu ga Ubanmu, dalilinsa.
A: Yesu ne Ɗan Allah, Shi ne ya panshe mu da jininsa.
K: Za ya ba mu tuta, za ya ba mu tuta, dalilinsa.
A: Yesu ne Ɗan Allah, Shi ne ya panshe mu da jininsa.
K: Za ya ba mu mulki, za ya ba mu mulki, dalilinsa.
A: Yesu ne Ɗan Allah, Shi ne ya panshe mu da jininsa.
K: Sai mu ɗebe shakka, sai mu ɗebe shakka, dalilinsa.
A: Yesu ne Ɗan Allah, Shi ne ya panshe mu da jininsa.
K: Sai mu yi da himma, sai mu yi da himma, dalilinsa.
A: Yesu ne Ɗan Allah, Shi ne ya panshe mu da jininsa.
K: Tabbata hakika, tabbata hakika, za ya ba mu mulki dalilinsa.