Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 456 Ku Zo Mu Bi Mai Ceto Lyrics
Ku zo mu bi Mai Ceto
Ko da shi ke duniya na kiranku,
Shi ne ya bada ransa
Don ya cece mu ya ba mu sabon rai
Wata rana za mu je
Ku zamna wurinsa
Ya kamata dai mu yi aniya cikin aikinsa
Ku zo mu bi Mai Ceto
Sa’anan mu yi murna har abada.