Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 454 Ku Yi Sowa Farin Ciki Lyrics
KORUS
Ku yi sowa farin ciki, duniya duka
Ga Ubangiji gama nagari ne shi.
1
Ku yi masa bauta da farin zuciya
Ku zo gabansa da rerawa
Ku sani Ubangiji shi ne Allah.
Shi ne yayi mu.
Korus
2
Ku sani Ubangiji ne ya yi mu
Ba mu ne muka yi kanmu ba
Mu ne mutanensa
Tumakin makiyaya tasa.
Korus
3
Ku shigo ƙofofinsa da godiya
Cikin harabunsa da rerawa
Ku yi masa godiya
Ku albarkaci sunansa
Korus
4
Gama Ubangiji nagari ne shi
Jinkansa madawami ne
Amincinsa ya tabbata
Daga tsara zuwa tsararaki.
Korus
