Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 452 Ku Tashi Dai Mutane, Ku Bi Ubangiji Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 452 Ku Tashi Dai Mutane, Ku Bi Ubangiji Lyrics

 

1
Ku tashi dai mutane
Ku bi Ubangiji
Ku tada tutar nasa
Tuta na shaidarsa
Zai ba mu nasara kuwa
Bisa magabcin mu
Har dukan mutanenmu
Su san Mai Cetonmu.

2
Ku tashi dai mutane
Ku yi biyayya kuwa
Ku shiga yaƙin Kristi
Ku bi Maganarsa
Kada ku koma baya
Amma ku ƙarfaffa
Don duniya za ta shuɗe
Duk da kwaɗayinta.

3
Ku tashi dai mutane
Ku shaida Bishara
Ta wurin ikon Yesu
Ku nuna ƙamnarsa
Ku yafa sulken kirki
Ku yi addu’a kuwa.
Har ran da Yesu Kristi
Zai ka mu gidansa.

Exit mobile version