Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 451 Ku Shiga Jirgin Yesu Lyrics
1
Ku zo ku kama hanya zuwa gidan Allahnmu
Ku shiga jirgin Yesu, ba za ku ɓace ba
Ku zo ku kama hanya, ku bar zunubanku!
Ta wurin jinin Yesu, ku sami cetonku.
2
Shi ne babban matuki, Shi ne Mai Cetonmu
Ya bada ransa duka don dukan ɓatattu.
Zai kai ku gidan Allah, ba za ku ɓace ba!
Zai cika ku da murna, rai na har abada.