Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 45 Ya Yesu, Muna Jiranka Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 45 Ya Yesu, Muna Jiranka Lyrics

 

1
Ya Yesu, muna jiranka,
Da ikonka na warkarwa.
Ba mu da ikon taimako.
Ka cika dukanmu yanzu.

2
Ka ji mu, muna nemanka.
Ba duk a nan sun san ka ba.
Mun sani kana nemansu.
Jawo su duk, Mai ƙaunarmu.

3
Kai ne mai sanin cutarmu,
Mai gyara mugun tunani.
Tone ƃoyayyun laifofi,
Mai Fansarmu kan giciye.

4
Ka cire ƙarin mutuwa,
Ka kau da aikin maciji.
A cikinmu, yi nasara
Don mulkinka madauwami.

5
Ka dubi masu ƙunci yau.
Rinjayi duk ƴan kangara.
Ka kwance ƙangin ɗaurarru,
Ka mai da su a hanyarka.

6
Ya Almasihu, Ɗan Mutum,
Ka ɗauki tabi’armu da,
Alherinka mai yawa ne,
Mai Cetonmu, Mai Gafara.

7
Kai ne da ikon warkarwa,
Da yau da kullum kamar da.
Ka ji mu yau, Maɗaukaki,
Warkad da mu da hannunka.

Exit mobile version