Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 449 Ku Dawo Lyrics
1
Idan mutanena waɗanda ake kira da sunana
Sun bar miyagun ayyukansu sun zo gareni
Ni zan ji in warkarda su
Ni zan ji in albarkace su.
KORUS
(Solo: “Ku dawo”
Ku dawo (2x
Don mi fa za ku mutu.
(bis
2
Hannuwan Ubangiji ba su gajarta ba da basu ceto
Kunnuwansa ba su yi nauyi
Ba da ba su jin addu’a
Zunubanmu sun hana Allah ya ji mu.
Korus
3
Abokin gaban mu yana so ya hallaka mu
Mu dawo wurin Ubangiji Allah mu roƙi gafara
Shi zai ji ya yi mana gafara
Shi zai ji ya bamu nassara
Korus