Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 447 Kowace Rana Akwai Jaraba Lyrics
1
Kowace rana akwai jaraba
zuwa ga dukan masu binsa
Duk da hakanan muna aniya,
ba za mu ba Shaiɗan dama ba.
KORUS
An jima za mu riƙa nasara.
Babu jaraba da za ta zo.
Mu tada muryar, mu yi waƙarmu.
Ba za mu ba Shaiɗan dama ba.
2
Lokacin da mutuwa ta sabko
ta ɗauki ƴaƴan tumakinmu,
Kada wannan ya sa mu ji tsoro.
Ba za mu ba Shaiɗan dama ba.
Korus
3
Bari mu mutu cikin hannunsa,
mu riƙe bangaskiyarsa sosai,
domin mu gaji mulki na sama
wanda Yesu yake shiryawa.
Korus
4
Mu tuna da ranar zuwan Yesu.
Duk masu bi za su yi murna,
kowace gwiwa za ta rusuna,
marasa bi za su yi kuka.
Korus