Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 442 Kasa Kunne Ga Labarinmu Lyrics
1
Kasa kunne ga labarinmu
Da cikin bauta mu ke,
Yesu ya zo daga can sama,
Ya cece mu, dukanmu.
KORUS
Wa ya wanke zunubai ?
Yesu ne akan giciye
Me ya yi mana? Ya mutu,
Ina ya ke ?
Yana sama, yana roƙo.
2
Ba mala’iku da za ya fi mu,
Kome daraja tasa,
An giciye shi, an rena shi,
Ɗaya ne cikin uku.
Korus
3
Za ka bada ranka gare shi
Ka durƙusa gabansa
Kai, kuma za ka ƙamnace shi
Shi kuma zai cece ka.
Korus