Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 441 Kasa Kunne Ga Gargaɗin Allah Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 441 Kasa Kunne Ga Gargaɗin Allah Lyrics

 

KORUS
Kasa kunne ga gargaɗin Allah yana gargaɗin masu bi
Kada ku yi tarayya fa tare da marasa bangaskiya
Ku fito daga cikinsu ku ware fa in ji Yesu
(Mutum 1 : “Kada ku”
taɓa kowane abu marar tsarki in karɓe ku
(Mutum 1 : “Ku zo ku”

1
Zama yaya maza da mata gareni
In ji Ubangiji shi mai iko duka
Ina gamin haikalin Allah da gumaka
Ina rabon mai bada gaskiya kuma ?
Wurin mara bada gaskiya in ji Yesu Mai Ceton duniya
(Solo : “Idan fa”
mutum yana cikin Almasihu Yesu
Tsofoffin ayyuka duka sun shuɗe fa
Sun zama sabobbi cikin Yesu.
Korus

2
Ayyukanmu a bayyane a wurin Allah mai iko duka
Fasakanci da kazamata Allah ba ya jin daɗin irinsu
Tsatsaguwa, kishi kishi, magabtaka da husuma
(Solo: “Irin su”

Ba za su shiga mulkin Allah Ubangijinmu ba
(Solo: “Don haka”

Korus

3
Ekklesiyar Almasihu mu bar aikata zunubi fa
Domin Allah Ubangiji sarkin saka ba ya kusantuwa
Shi wanda zakin idonsa ba ya kallon shirinka
(Solo: “Abinda”
Allah ba ya so shi ne zunuban da mu ke yi
(Solo : “Lallai ne”

Korus

Exit mobile version