Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 44 Zo, Mu Kawo Kukanmu, Yesu Yana Jiranmu Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 44 Zo, Mu Kawo Kukanmu, Yesu Yana Jiranmu Lyrics

 

1
Zo, mu kawo kukanmu, Yesu yana jiranmu,
Shi da kansa ba ya ƙi, yana so ya riƙa ji.

2
Shi ne Sarkinmu babba, mu ba za mu rasa ba.
Kome yawan roƙonmu, shi zai biya bukatarmu.

3
Ga ni nan mai zunubi, Almasihu, sai ka ji.
Cikin ikon jininka, kau da kayan laifina.

4
Ina neman hutawa, zo, ka shigo zuciyata.
Karƃi mulki, kai kaɗai, babu sarkina, sai kai.

5
Cikin duniyan nan yanzu, Yesu, kana bi da mu.
In mun gama aikinka, sai ka kai mu gidanka.

Exit mobile version