Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 437 Kai Ne Mai Zuwa Nan Lyrics
KORUS
Kai ne mai zuwa nan
Ko mu jira wani
Ko kai ne shafaffen nan na Allah
Kai ne Almasihu ko mu jira wani.
1
Ku je ku shaida, ku je ku faɗi
Abin da kuka gani da abin da kuka ji
Ga makafi na gani, kurame na ji
Albarka ga wanda bai samu sanadin tuntuɓe wurina.
Korus
2
Ku je ku shaida, ku je ku faɗi
Abin da kuka gani da abin da kuka ji
Ga guragu na tafiya, kutare na tsarkaka
Albarka ga wanda bai samu sanadin tuntuɓe wurina.
Korus
3
Ku je ku shaida, ku je ku faɗi
Abin da kuka gani da abin da kuka ji
Ga matattu na tashi, bishara ga talakawa
Albarka ga wanda bai samu sanadin tuntuɓe wurina.
Korus
