Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 436 Kafin Ya Hau Sama Lyrics
KIRA: AMSA:
1
Kafin ya hau sama….ya koya masa abubuwa
Wadada zasu faru….a kwanakin karshe
Illimi zata karu….son kuɗi zata karu
Yaya zasu zama da taurin kai….ga iyayensu
Ka’a yi yakoki….a karshen duniya
Amma mu masubi….muyi zaman tsaro (2x
KORUS
Wai yo….tuna fa…zamanin nan ta karshe ce
Dawowa (Bass
Yesunmu….Hakika yayi kusa
Wai yo…ah..ha….Ƴan’uwa sai muyi lura
2
Jin dadin duniya nan….ya dauki hankalinmu
Wasu sun malake ta….sun manta da mutuwa
Sai shagalin duniya….nan kasar kwanakin Nuhu
Wasu suna takama….suna iko da duniya
Randa kwana ta kare….ai ya abin tausayi (2x
Korus
3
Kome da muke aikata…..a wannan duniya
Adalci ko mugunta….akwai ranata karshe
Wata rana farat ɗaya….Mallam sai labari
Allah mahalicinmu….ba’a yi masa ba’a
Abin da mun shuka….lallai zamu girba (2x
Korus
4
Ƴan’uwan masubi….muyi zaman tsaro
Bamu san rana ko sa’a….randa Yesu zaya zo
Mike bagaskiyanmu….banda sakaci ba
Kada wannan rana….fata hume mu
Karshen abu duk….inji Sarkin Suleyman
Mu ji tsoron Allah….mu aika ta nufinsa (2x
Korus
