Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 435 Kada Zuciyarku Ta Ɓaci Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 435 Kada Zuciyarku Ta Ɓaci Lyrics

 

1
Kada zuciyarku ta ɓaci
In ji Yesu Kristi.

2
Gama za shi sama
Za ya shirya wuri can.

3
Za ya sake zuwa
Domin ya karɓe mu.

4
Mu shirya zukatanmu
Domin ranar zuwansa.

5
Kai, mai bi a karkace
Sai ka gyara zamanka.

6
Kau da duka tsafinka
Idan kai mai bi ne.

7
Idan yau da tsafin nan
Allah yana kishinsa.

8
Idan kana da laya
Allah yana kishinsa.

9
Rabu da waɗannan duka
Ko dogara ga Allah.

10
Sai ka fara bidan
Mulkin Allah yanzu.

11
Domin ka sami rai
Cikin Yesu Mai Ceto.

12
Za mu zamna can a sama
Cikin gidan Allah.

13
Daɗin, daɗi za mu ji
Can tsare da Yesu.

14
Murna, murna za mu yi
Can a gidan Allah.

Exit mobile version