Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 43 Yi Addu’a, Ba Fasawa Lyrics
1
Yi addu’a, ba fasawa,
Kullayaumin ka yi addu’a.
Duk ka roƙa Allah ya ji.
Ba ya ta da alkawari.
2
Yi addu’a, ba fasawa,
Ba kankanta a idonsa.
Buɗe zuciya a gabansa,
Yi addu’a, shi ne mai ji.
3
Yi addu’a, ba fasawa,
Kada Mugun ya yi nasara.
Yesu wanda an jarraba
Zai riƙe ka, ka yi addu’a.
4
Yi addu’a, ba fasawa,
Ko da ƙunci ya danne ka.
Ba ya kyale wahalarka,
Zai daidaita, ka yi addu’a.
5
Yi addu’a, ba fasawa,
Kwanciyar ranmu sai bangaskiya.
Allah shi ne mai amsawa,
Dole kullum mu yi addu’a.