Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 426 Ina Tafiyar da Ubangiji Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 426 Ina Tafiyar da Ubangiji Lyrics

 

1
Ina tafiya da Ubangiji
Shina bishe ni ga duk hanyoyi
Zama da shi ba kamar na mutum
Murna, salama da kwanciyar rai.

KORUS
Na fa son wannan zama da irin na duniya
Da zaman nan na banza da yabon mutane
Marmarina in gamshe shi kowane lokaci
Muna tafiya bisa, bisa zuwa gidanmu.

2
Ga shi nan kusa, Mai taimakona
Shina riƙe da hannuna dama
Kullum fa shina ta ƙarfafata
Lokacin murna ko na wahala.
Korus

3
Har ya ɗauke ni, ya kai ni sama
Ina tafiya da Ubangiji
Murna ta cika, za ga fuskarsa
Da duk annabawa da duk masu bi.
Korus

Exit mobile version