Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 424 Ina Farin Ciki Lyrics
KORUS
Ina farin ciki tare da waɗanda suka ce mani
Ku zo mu je gidan Ubangiji. (3x
Ƙafafun mu suna tsaye
Cikin ƙofofinki Urushalima.
1
Kursiyai ma, nan suke
Kursiyai na shari’a
Kursiyai na gidan sarki
Dauda suma nan suke.
Korus
2
Kabilu duka nan suke
Kabilu na Ubangiji
Domin su ɗaukaka sunansa
Mai tsarki bisa ga dokokinsa.
Korus
3
Ku yi addu’a
Domin salamar Urushalima
Waɗanda suke ƙaunarki
Urushalima su yi addu’a.
Korus