Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 422 In Na Sami Dukan Kome na Duniya Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 422 In Na Sami Dukan Kome na Duniya Lyrics

 

1
In na sami dukan kome na duniya
Wannan da amfani ne, in ba ni da ceto?
A cikin zuciya in ba salama
Me za a yi da kayan duniya?
Ko na sami duniya, amma ba ceto
Gwamma ba a haife ni da na shiga Jahanama.

KORUS
Ba ni Yesu, O ba ni Yesu
Kullum, har abada, O ba ni Shi.

2
Ko na sami dukiya cikakkiya
Da suna sannanu ga dukan mutane
Amma babu bege ko wurin sabka
Ina amfaninsu a sa’annan?
Ba shakka Allah ba zai yi wargi ba.
Yanzu ka taimake ni in yi tunani.
Korus

3
Duk walaha ce in ba tare da Yesu
Ɓatace ne ni cikin zunubaina
In har abada ba ganin haske
Dufu kaɗai da zafin kuka
Ko na zama nan ba bukatar Yesu
Ran da na mutu fa, ina dabarata?
Korus

4
Murna ba misalinta wurinsa
Maganin baƙin ciki, ɓa’a azaba
Ba zunubi da ya ƙi yin wanke
Ko wahala da ba za ya ji.
In na zama ni kaɗai da Yesu
Ba kome ba ne, shi ne bukatata.
Korus

Exit mobile version