Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 421 In Ji Mai Cetona Lyrics
1
In ji Mai Cetona
Kai ba ka iya ba
Ni kaɗai Mai Cetonka
Zan biya laifinka.
KORUS
Shi ya biya duk
Ni mai bashi ne
Shi ya zubda jininsa
Ya wanke zuciyata.
2
Jinin Ubangijina
Jininsa ne kaɗai
Ya wanke zuciyata
Ya biya bashina.
Korus
3
Ikon Yesu shi kaɗai
Zai sake halina
Ni ban iya kome ba
Shi kaɗai Mai bada rai.
Korus
4
Ran da zai dawo dai
Zan tsaya gabansa
Ba zan ji tsoro ba
Don ya biya laifina.
Korus