Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 413 Ga Mutum Mai Ƙazamin Ruhu Lyrics
1
Ga mutum mai ƙazamin Ruhu
Ya gamu da Yesu dai
Kullum kuwa ko dare da rana
Yana kururuwa dai.
Ya tsatsage jikinsa kuwa
Can kabari da duwatsu.
2
Ba wanda na da iko shi damre
Mai ƙazamin Ruhun nan
Sau da yawa ya tsutsunke
Har sarƙoƙi ya karye su.
3
Sai ya iske Yesu na zuwa
Daga nesa ya iske shi
Ya sheƙo a guje domin
Ya yi masa sujada fa.
4
Ya ce “ina ruwana da kai,
Yesu kai Ɗan Allah ne ?”
Ya ce “Ka fito daga cikin
Mai ƙazamin Ruhun nan.”
5
Ҡazamin ruhohin nan
Sun shiga cikin gursunnai
Su sun faɗi cikin teku
Sun nutse dai, sun shaƙe kuwa.
6
Ta wurin ikon Maɗaukaki
Yesu Ɗan Allah kaɗai
Mai ƙazamin ruhun ya zama
Mai hankali, mai shaida kuwa.
7
Sai mu bi Yesu don ya iya
Cece mu daga Shaiɗan.
Mu gaskanta shi Ɗan Allah ne
Mai Cetonmu, Mai Kamnarmu.
