Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 41 Ya Ubangijinmu, Muna Yin Addu’a Lyrics
1
Ya Ubangijinmu, muna yin addu’a
Kai kaɗai mai iko, kasa mana kunne.
2
Ba mu isa ba fa, kasassu ne duka,
Amma muna duban Yesu Almasihu.
3
Cikin sunan Yesu, ga mu nan gabanka.
Dukanmu mun taru garin yin sujada.
4
Kai kaɗai mai iko, kai kaɗai mai sani.
Tunanin zukata, bincike su duka.