Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 409 Ga Allah Kaɗai, Mahiliccinmu Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 409 Ga Allah Kaɗai, Mahiliccinmu Lyrics

 

1
Ga Allah kaɗai, Mahiliccinmu,
Daidai mu yi waƙar yabonsa yanzu.

KORUS
Mu yi waƙar yabon Allah
Addu’ar za mu yi.
Mu yi waƙar yabon Allah,
Mu girmama shi.

2
Mu girmama shi, addu’ar za mu yi.
Mai kyauta ba gori duk baiwa sai shi.
Korus

3
Mai raya mutum kyautar, Allah sosai
Ban da Allah, ina za mu sami jinƙai?
Korus

4
Jinƙai ne ya sa ya yi mana baiwa
Da ya aiko Mai Ceto tun zamani dā.
Korus

5
Mai Ceto ne shi wanda Allah ya ce
Shi Ɗansa ne, ransa ya so shi sarai.
Korus

6
Labarin Mai Ceto da daɗi ya ke
Mutuwassa da tashinsa duk namu ne.
Korus

7
Duk wanda ya ce Almasihu zai bi,
Tsattsarken numfashi zai ƙarfafa shi.
Korus

Exit mobile version