Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 408 Ga Alkawari na Allah Cikin Littafi Mai Tsarki Lyrics
1
Ga alkawari na Allah cikin Littafi Mai Tsarki
Yesu ya yi mani shi
In kun roƙi kome ne. A cikin sunana dai-dai
Shi zai ji addu’arka.
KORUS
Yesu yana jiranmu mu zo gareshi
Kome ya ke damunka
Tashi dai ka yi addu’a
Wanda ya zo gunsa, za a taimake shi,
Lalle yana jin addu’a.
2
Dukan inda biyu ko uku suna nan a tattare
Nan ya ke a tsakiya
Dukan wanda ya yi roƙo tare da bangiskiya
Za a ji addu’arsa.
Korus
3
In na kiyaye mugunta a cikin zuciyata
Allah ba zai ji ni ba,
Addu’ar mai ƙin shari’a abin ƙyama ne ya ce,
Allah ba zai ji ta ba.
Korus
4
Bari dai mu yi addu’a kullum ba da fasawa
Domin duka tsarkaka,
Mu yi tsaro fa a ciki, mu yi tare da godiya
Allah yana jin addu’a.
Korus