Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 401 Dare Ya Yi, Baitalahmi Lyrics
1
Dare ya yi, Baitalahmi, mutane sai barci,
Sai makiyaya can daji, suna lura da tumaki
Sai mala’ika ya zo, sai mala’ika ya zo.
2
Kada ku ji tsoro, ga shi, na kawo labari
Gama yau cikin Baitalahmi an haifa maku Maceci,
Ɗan jariri ne shi, ɗan jariri ne shi.
3
Nan da nan, daga can, runduna na sama
Suna yabon Maɗaukaki, suna murna da farin ciki
Yau Mai Ceto ya zo, ya Mai Ceto ya zo.