Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 40 Ya Uba Na Cikin Sama, Ina Roƙonka Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 40 Ya Uba Na Cikin Sama, Ina Roƙonka Lyrics

 

1
Ya Uba na cikin Sama, ina roƙonka,
Bisa ga alkawarinka, ji addu’ata.

KORUS
Yesu, Yesu, ji addu’ata,
Ina zuwa wurin Uba cikin sunanka.

2
Uba, ga ni nan gabanka, na yi zunubi.
In ba za ka karƃe ni ba, wa zai taya ni?
Korus

3
Cikin ƙasar can mai nisa, na yi baƙunci,
Amma dai yanzu na komo, sai ka karƃe ni.
Korus

4
Ni ban isa ba ka ji ni, Allah Ubana,
Amma cikin sunan Yesu, kawo gafara.
Korus

5
Uba, ina yin godiya, kai ka karƃe ni.
Ka maishe ni bawa naka, aikinka in yi.
Korus

Exit mobile version