Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 398 Daga Ina Ne Cetona Zai Zo Lyrics
1
Daga ina ne cetona zai zo
Daga Ubangiji sarki mai daraja
Daga Ubangiji babban marayu
Cetona zai zo.
2
Daga El-shaddai wato Allah mai iko duka
Jehovah Rapha Allah mai warkasuwa
Jehovah Jire Allah mai tanadawa
Cetona zai zo.
3
Daga El-Elyon wato Allah Maɗaukaki
Jehovah Nisi Allah ne tutata
Jehovah Ra’ah Allah Makiyayi
Cetona zai zo.
4
Daga Adonai wato Allah Ubangiji
Jehovah Shalom Allah ne salamata
Jehovah Saba’oh Allah mai runduna
Cetona zai zo
5
Daga El-Hai wato Allah ne rayayye
Jehovah Mekoddishkem Allah Mai Tsarkakewa
Jehovah Shammah Allah yana nan
Cetona zai zo.
