Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 397 Da Yesu Za Mu Kwana Lyrics
1
Da Yesu za mu kwana, da shi za mu tashi,
Za mu yi yabonsa don shi ne makiyayi.
Idan za ka tsira, sai dai ka bi shi.
Maida saura baya. Yesu ya fi su girma.
2
A can sama da daɗi, can za mu huta.
Za mu ga Ubanmu, mu yi masa sujada.
Shaiɗan da saura za su sha azaba.
Za su yi ta kuka. Yesu ba zai kula ba.
