Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 395 Cikin Wata Na Shidda Lyrics
1
Cikin wata na shidda (3x
An aiko Jibra’ilu. (3x
Cikin wata na shidda
An aiko Jibra’ilu.
2
Zuwa wani birni (3x
Sunansa Nazaret. (3x
Zuwa wani birni
Sunansa Nazaret.
3
Zuwa ga budurwa (3x
Sunanta Maryamu. (3x
Zuwa ga budurwa
Sunanta Maryamu.
4
Ya ce, za ki yi ciki, (3x
Cikin kuwa ruhu ne (3x
Ya ce, za ki yi ciki.
Cikin kwa ruhu ne.
5
Maryamu ta ce masa (3x
Ga ni kwa baiwa ce (3x
Maryamu ta ce masa
Ga ni kwa baiwa ce.
6
Maryamu ta haifi ɗa (3x
Sunansa Yesu ne (3x
Maryamu ta haifi ɗa
Sunansa Yesu ne.
7
Maryamu ta haifi ɗa (3x
Kamar ɗan talaka. (3x
Maryamu ta haifi ɗa
Kamar ɗan talaka.
8
Ashe ɗan sarki ne. (3x
Ya zo ya cece mu. (3x
Ashe ɗan sarki ne.
Ya zo ya cece mu.
9
Mu kuwa muna murna, (3x
Domin ya cece mu. (3x
Mu kwa muna murna,
Domin ya cece mu.