Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 392 Ceto Gun Yesu Lyrics
1
Lokacin da na faɗa cikin jaraba
A cikin hannun magabci Shaiɗan
Ni kan daga hannuwana a sama
Inda cetona zai fito.
KORUS
Ceto gun Yesu, jinƙai ga Allahnmu
Nassara, salama, suna cikin hanyar Yesu
2
Don mine ne kake tagumi ya raina
Don mine ne kake alhini a cikina
Ka kafa bege ga Allahna
Inda cetona zai fito.
Korus
3
Lokacin da na yi kuka ga Allahna
Lokacin da na yi ƙara ga kunnensa
Lokacin da na kawo damuwata
Allah ya ji ya ceci ni.
Korus
4
Albarka ta tabbata ga Ubangiji
Zan yabe shi dare da rana
Mutane ku zo mu tarbi Ubangiji
Inda cetonmu zai fito.
Korus